Labarin yadda ƴan sanda suka kama matar da ke safarar makamai ga ƴan ta’addan jihar Zamfara

Ƴansanda sun kama wata mata da ke safarar makamai ga ƴan ta’adda a Zamfara

https://apahausa.com.ng/video-kai-jamaa-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-koma-tamkar-indiyawa/

Rundunar ƴansanda a jihar Zamfara ta ce jami’anta sun kama wata mata mai suna Fatima Sani bisa zarginta da hannu wajen safarar makamai ga wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar.

The Cable ta rawaito cewa, da ya ke magana a wani taron manema labarai a jiya Juma’a, mai magana da yawun rundunar ƴansanda a Zamfara, Muhammed Shehu, ya ce an kama wacce ake zargin ne bayan samun bayanai a kan ta.

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4an-bindiga-ke-lalata-ta-matan-mutane/

“A ranar 13 ga Fabrairu, 2023, jami’an ‘yansanda sun kama wata r da aka ambata a sama dauke da harsasai har guda 325, biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da ita a garin Lafia a jihar Nasarawa zuwa ga wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a dajin Zamfara. ,” inji shi.

“A yayin da ake yi ma ta tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ta shiga sana’ar ne kuma a baya ta yi safarar bindigu kirar AK-47 guda uku da kuma harsashi 1,000 na AK-47 ga ‘yan bindiga da ke aiki a Zamfara.”

Views: 30

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *