Labarin yadda matashi ya mance hanyar zuwa garinsu bayan shefe shekaru 24 a gidan yari

Yadda Wani Mutum Ya Manta Hanyar Zuwa Garinsu Bayan ya Shafe Shekaru 24 a Gidan Yarin Imo

Sunday Ogbuo, dan asalin UmuochubaAgba, Ekwulobia, a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra, ya manta da hanyar garinsu, bayan ya shafe shekaru da dama a gidan yari na hukumar gyaran hali na Najeriya.

https://apahausa.com.ng/video-kai-jamaa-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-koma-tamkar-indiyawa/

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya nuna Mista Ogbuo, yayin da wasu mutane ke tattaunawa da shi, inda suka gan shi ya makale a wata mahadar mota a jihar Imo bayan an sako shi daga gidan yari.

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4an-bindiga-ke-lalata-ta-matan-mutane/

A cewar Mr. Ogbuo, ya kasance a gidan yarin jihar Imo tun a shekarar 1999, amma lauyoyin kare hakkin dan Adam sun saka baki an sake shi daga gidan yari a ranar Laraba 14 ga watan Yuni 2023; daga nan sai ya fara neman hanyarsa ta komawa garinsu Ekwulobia a jihar Anambra, kafin wasu Samariya suka gan shi.

A yayin da sukayi hira dashi ya sanar da su cewa ya manta hanayr zuwa garinsu.

Daga Baba Waziri Net

Views: 31

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *