“TALAUCI:Yadda wasu Iyalai suke Rayuwa cikin Kwalbati da tarkace a ƙasar Philippines

TALAUCI: Yadda Iyalai Suke Rayuwa Cikin Kwalbati Da Tarkace A Kasar Philippines.

Hotuna masu ban tausayi suna iyalai su na Rayuwaa cikin Kwalbati da cikin tarkace na Birnin Manila na Kasar Philippines 🇵🇭

Hotunan sun nuna iyalai da suka yi gidaje a cikin Kwalbatin siminti da ke kan titunan Manila

Za a iya ganin matasa har da jarirai suna barci a cikin sharar da Hotunan sun nuna iyalai da suka yi gidaje a cikin Kwalbati da ke kan titunan Manila

Kusan kashi ɗaya bisa huɗu na ƙasar suna rayuwa cikin talauci, wanda aka ayyana a matsayin rayuwa akan kusan dalar Amurka ɗaya a Rana.

Amma ga matalautan Philippines, suna ganin Wannan itace mafaka da zasu iya samu. Ana iya ganin iyalai suna barci da matsuguni a cikin Kwalbati da ke kan titunan Manila yayin da yara ƙanana ke wasa a ƙasa mai Dauke da ƙazanta.

Yawancin ƴan ƙasar Philippines da ke da Cikin matsananciyar wahala suna zama a cikin kowane matsuguni na wucin gadi da za su iya samu a cikin ƙauyen Manila.

Philippines ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe mafi saurin bunƙasa tattalin arziki a Asiya tsawon shekaru da yawa.

Sai dai duk da kokarin da gwamnati ke yi na inganta rayuwa, kasar mai Mutane sama da miliyan 100 har yanzu tana fuskantar manyan kalubale da suka hada da ga guguwa da sauran bala’o’i, talauci, cin hanci da rashawa da rashin ababen more rayuwa.

Kusan kashi ɗaya bisa huɗu na al’ummar ƙasar na rayuwa cikin talauci, wanda aka ayyana a matsayin rayuwa akan kusan dalar Amurka ɗaya a rana, a cewar bayanan gwamnati.

Kasar Philippines tana fuskantar matsakaitan mahaukaciyar guguwa Sau 20 a duk shekara, da yawa daga cikinsu suna yin kisa, inda mafi karfi ke faruwa a karshen shekara.

Daya daga cikin ta baya-bayan nan ita ce Guguwar Typhoon Melor a watan Disamba, wadda ta kashe akalla mutane 11 tare da yanke wutar lantarki ga miliyoyin mutane.

Kuma watanni biyu kacal kafin wannan, dubun dubatar mutane sun rasa matsuguni bayan da guguwar Koppu mai karfin gaske ta afkawa arewa maso gabashin Philippines.

Guguwar mai karfin gaske ta zagaya tsibiran inda ta lalata gidaje tare da Karya bishiyoyi da layukan wutar lantarki tare da farfasa hanyoyi da gadoji.
Fassarar Saliadeen Sicey

Source Alfijir hausa

Views: 42

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *