VIDEO: “Mutumin da ya ƙone Alƙur’ani a Swedin Salwan Momika yayi alƙawarin ƙara ƙona wani”

INNALILLAHI WA’INNA LLAIHI RAJI’UN: Bayan Gabatar Da Kona Al-qur’ani A Kasar Sweden, Salwan Momika yayi alkawarin Kara Kona wani Al-qur’ani Mai girama.

Makiyin Musulunci Salwan Mika, Haifafen Kasar lraq shine ya kona Al-qur’ani Mai girama a wajen Babban Masallacin Stockolm wato babban birnin kasa Sweden.

Kona Al-qur’anin ya faru ne yayin da musulmai ke bikin ldin Babbar Sallah a ranar Larba da ta gabata.

Momika ya bayyana Al-qur’ani a Matsayin littafin dake tauye hakki da Dimokuradiyya.

Sai dai da yawa Yan Kasar Sweden basu yarda da Matakin ba, har ta Kai wasu Sunyi zanga-zangar tare da bayyana abinda momika ya yi a Matsayin tada zaune tsaye.

Duk da rashin amincewa da matakan Salwan momika ya Kuma you Alkawarin Kara Kona wani Al-qur’ani Mai girma a Nan gaba.

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *