Yadda gobara ta jawo asarar miliyoyi a kasuwar Albasa dake jihar Sokoto

Photon Wani Mai Siyar Da Albasa

Rahotanni daga jihar Sokoto, sun tabbatar da cewa Gobara ta jawo asarar miliyoyin kudade, a kasuwar yan Albasa da ke jihar wani rahoto ya bayyana cewa, “Gobara a kasuwar albasa a Ramin Kura da ke jihar Sakkwato ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin nairori ga manoma”.

Yadda Albasar Ta lalace

Kawo wannan lokaci dai babu rahotan jikkata ko asarar rai a sanadiyyar ta shin wannan gobara, in banda asarar da ta jawo wa manoman albasar kamar yadda rahotanni suka nuna, jihar ta Sokoto dai ta sha fama da gobara a cikin kasuwannin jihar.

Ko a farkon shekarar nan ma saida gobara ta jawo asarar dubban miliyoyi a babbar kasuwar jihar. Muna fatan Allah ya kiyaye faruwar wannan al’amari a nan gaba ameen.

Views: 49

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *