Yadda hukumar ICPC ta bankaɗo jami’an wani banki suna ɓoye sabbin kuɗaɗe

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (ICPC) ta sake bayyana cewa; bankuna na da sa hannu akan ƙarancin sababbin kuɗaɗe.

Hukumar (ICPC) ta wallafa wani faifan bidiyo wanda yake ɗauke da sababbin kuɗaɗe da aka ɓoye a banki.

‘Yan Najeriya sun mayar da martani yayin da babban bankin kasar CBN ya hada hannu da ICPC da sauran hukumomin kudi da tsaro domin magance matsalar ƙarancin sababbin kuɗaɗe.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta gano wasu tarin sabbin takardun kudi na Naira da aka boye a cikin wata ma’ajiya a banki.

A cikin wani faifan bidiyo da hukumar ta wallafa a shafin ta na twitter domin tabbatar wa jama’a a ranar Asabar, 4 ga Fabrairu, 2023, an ga jami’an hukumar suna ba da umarnin wani jami’in banki da ya fito da kuɗaɗen.

A halin da ake ciki, ICPC ta yi alƙawarin murkushe abubuwan da ke kawo cikas ga ƙoƙarin samar da takardar kuɗin Naira da aka sake fasalin ga jama’a.

Tuni dai aka kama wasu jami’an bankin kasuwanci bisa zargin yin zagon kasa kuma ana sa ran za a kama wasu a cikin kwanaki masu zuwa.

© twitter247 Nigeria News Update.

Views: 31

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *