Yadda makwafci ya kama makwafcinsa na leken matarsa tana wanka a ban daki

Rahotanni daga jihar Benue na cewa wani makwafci mai suna Salahu ya kama makwafcinsa yana leken matarsa tana wanka a ban daki inda ya mika shi hannun jami’an tsaro.

Lamarin wanda ya faru a safiyar ranar Asabar dai dai lokacin da matar mai suna Humaira ke wanka a ban daki idan shi kuma mai gidan ya fita waje kawai sai yaga makwafcinsa yana leken matarsa tana wanka a ban daki.

A lokacin da lamarin ya faru mutanen unguwar sun nemi mai gidan ya bari su lakada masa duka amma ya ce a’a a mika shi ga jami’an tsaro domin a hukunta shi, rahoton ya kara da cewa dama mutumin ana zarginsa da haura katangar matan mutane musamman matan da ya san cewa mazajensu sunyi tafiya.

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *