Yin tattaki a kullum na kare haɗarin mutuwa da wuri—Bincike

Yin tattaki a kullum na kare haɗarin mutuwa da wuri –

Ba wai sai ka kasance ɗan tsere ba ko kuma mai harkar wasu wasanni ba domin cin moriyar alfanun motsa jiki – soma yin tattaki a kowace rana ya wadatar, kamar yadda wani nazari da aka yi a Birtaniya ya nuna.

Nazarin ya gano cewa idan mutum zai yi tattaki na aƙalla minti 11 a kowace rana, hakan na iya rage haɗarin mutuwar wuri ta mutum ɗaya cikin 10.

Akasarin mutane ba sa iya samun damar motsa jiki duk mako na tsawon minti 150 da aka bayar da shawara.

Amma ko ba komai gara a ce mutum yana motsa jikinsa maimakon a ce ba ya yin komai, in ji masu binciken daga Jami’ar Cambridge.

Hukumar Lafiya ta Birtaniya, NHS ta bayar da shawarar kowane mutum ya riƙa motsa jiki na tsawon minti 150 zuwa 300.

Wanda a cewarta hakan zai ƙara bunƙasa lafiyar zuciya kowane mako.

Ko kuma motsa jiki tuƙuru na tsawon minti 75 zuwa 150 a kowane mako, wanda hakan ke ƙara lafiyar zuciya ta hanyar inganta numfashi.

Tawagar masu binciken ta duba wasu nazarce-nazarce da aka yi a baya game da alfanun motsa jiki.

Bisa wannan binciken ne ta yanke shawarar cewa yin rabin abin da aka bayar da shawara, na iya kare mutum ɗaya cikin ashirin daga cututtukan zuciya da kuma kusan mutum ɗaya cikin 30 masu fama da cutar daji.

Hakan ya yi dai-dai da minti 75 a kowane mako – ko kuma minti 11 a kullum – tuƙa keke da yin tafiya da sauri ko hawa tsauni ko rawa ko kuma yin wasan ƙwallon tennis”

Dr Soren Brage, wanda ya jagoranci binciken ya ce “ya kamata ku ji jikinku na motsi, zuciyarku na bugawa da sauri amma ba lalle ku ji numfashinku ya ɗauke ba.”

Yin hakan daidai yake da rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya da shanyewar ɓarin jiki da kashi 17 cikin 100 da kuma cutar daji da kashi bakwai cikin 100, kamar yadda binciken ya nuna.

Motsa jiki a kai-a kai yana rage yawan kitse a jiki da kuma ƙara yawan jini yayin da kuma yake inganta lafiyar jiki da bacci da na zuciya na tsawon lokaci.

Source: bbchausa

Views: 32

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *