Ƙasashen larabawa sun daina siyan kayan ƙasar Indiya saboda kisan musulman da take yi

Kisan da ƙasar Indiya ke yiwa al’ummar musulmi ta sa ƙasashen Larabawa sun daina siyan kayan da ƙasar ke fitarwa.

An fara kaddamar da kamfen na kauracewa kayayyakin kasar India a shafukan sada zumunta a yankin Gabas ta Tsakiya. Kauracewa kayayyakin kasar wani yunkuri ne na nuna zanga-zangar adawa da zaluncin da ‘yan sanda suke yiwa daruruwan Musulmi a yankin Assam dake Arewa maso Gabashin kasar a watan jiya.

Baya ga wannan zanga-zanga da aka fara kan rashin imanin kasar ta Indiya, hashtag na #India_Kills_Muslims yayi shuhura sosai a shafin Twitter, bayan mutane sun yi ta kira akan kisan kiyashin da kasar India ke yiwa Musulmi.

Wannan lamari dai ya faru ne, bayan gwamnati ta sanya ‘yan sanda su rushe sama da kilomita 100 a yankin Assam, wajen da wasu Musulmai ke zama ba bisa ka’ida ba.

Kasar dai ta yi ƙaurin suna wajen take hakkin bil’adama musamman ga Musulman kasar.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *