Ƴan luwaɗi sun fi masu yin Mauludi tsafta—Sheikh Anas Ghana yayi ƙarin haske

Shafin Labarun Hausa ya ruwaito cewa.

Tun farkon makon nan malaman izala da na darika suke ta cece-kuce akan furucin Sheikh Anas Taufiq Ghana wanda ya ce Luwadi ya fi tsafta akan Maulidi.

An samu wadanda su ke goyon bayansa dari bisa dari yayin da wasu suka dinga sukarsa bisa ruwayar Tashar Tsakar.

Hakan ya biyo bayan yadda wasu malaman izala suka dinga sassauta ra’ayinsu dangane da

Malaman sun hada da su Malam Nura Khaleel da sauransu inda su ke cewa ya kamata a sassauta tsanar da ake nunawa ga masu Maulidi don gudun jefa mutum ga kin ma’aiki.

Shi kuwa Sheikh Anas Taufiq yayin nuna tsantsar haramcin Maulidi ya yi furuci mai muni wanda ake ta cece-kuce akai kusan makwanni 2 kenan.

Bayan jin yadda mutane su ka dinga sukar sa, malamin ya dawo ya sake bayani dangane da furucin nasa,
inda ya ce.

Ya ce akwai manyan malamai da suka goyi bayan wannan maganar tasa. Inda ya kafa hujja akan yadda masu maulidi wanda ya ce bidi’a ne ba sa tuba.

A bangaren mazinata da masu luwadin da suke tuba kuma Ubangiji zai yafe musu Shehin Malamin ya ce sun fi tsafta.

Don haka ya ce masu tuba duk da sun yi luwadi ko zina sun fi masu maulidin da basa tuba tsafta a wurin Allah.

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *