Ƴan Sandan Najeriya Sun Bindige Ɓarawon Akwatin Zabe A Kogi

Yan Sandan Najeriya Sun Bindige Ɓarawon Akwatin Zabe A Kogi

Yan daba sun yi yunkurin kwace akwatin zabe a karamar hukumar Dekina, jihar Kogi.

Wakilin ALFIJIR HAUSA ya Shaida mana Cewa; An kashe wani dan daba mai Kimanin Shekaru 36 yayin da wasu suka samu raunuka lokacin da suka yi arangama da wasu Yan Sandar Najeriya a Ƙoƙarin su na Sace Akwatin Zabe.

Sai dai har yanzu Wakilin namu yace; ba’a iya tantance ko yan wani Jam’iyyar bane Yan daban Suka kawowa rumfar zaɓen hari da Sunan yin awon gaba da Akwatin Zabe.

Views: 15

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *