Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Legas
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da sakamakon wucin-gadi na zaɓen shugaban ƙasa a jihar Legas, inda ta nuna cewa jam’iyyar Labour, wadda Peter Obi ke yi wa takara ce a kan gaba.
To amma akwai buƙatar sai hukumar zaɓe ta ƙasa a matakin tarayya ta tabbatar da sakamakon kafin ayyana wanda ya yi nasara.
Ga yadda hukumar INEC ɗin ta bayyana sakamakon a birnin Legas:
Masu kaɗa ƙuri’a da aka tantance: 1347152
APC: 572,606
LP: 582,454
NNPP: 8,442
PDP: 75,750
Wannan ne sakamakon da INEC za ta kai cibiyar bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Abuja.
source: bbchausa
Views: 17
