2023: Obasanjo ya bayyana Obi a matsayin ɗan takarar da zai goya wa baya

2023: Obasanjo ya bayyana Obi a matsayin ɗan takarar da zai goya wa baya

A karshe dai, tsohon shugaban kasa,
Olusegun Obasanjo, ya fito fili ya nuna goyon bayan sa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

DAILY NIGERIAN ta samu labarin cewa Obasanjo ya dade ya na tallata takarar tsohon gwamnan jihar Anambra a asirce, inda ya riƙa haɗa Obi da manyan ƴan siyasa.

A cikin sakonsa na sabuwar shekara ta 2023 da shi da kansa ya sanya wa hannu, Obasanjo ya bayyana Obi a matsayin ɗalibin sa a siyasa, ya na mai cewa ga dukkan alamu Obi ne zai samu nasarar lashe zaɓen a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

“Babu wanda ba shi da laifi a cikin ƴan takarar amma idan aka yi duba da halayya, tarihi, fahimta, ilimi da nagarta da za su iya kawowa da kuma babban kokarin da ake bukata don ci gaba da mai da hankali kan aiki, duk Obi ya fi su. A gogewar aikin da ni da kaina nake da ita, Peter Obi dalibi na ne,” in ji Mista Obasanjo.

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *