Nayi iya bakin ƙoƙarina a mulkin ƙasar nan amma ƴan Najeriya basu gani—Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa a mulkin ƙasar nan daya shafe tsawon shekaru 8 yana jagoranta.

Kamar yadda ya bayyana Buhari yace ba lallai aga ƙoƙarin da ya yi ba a halin yanzu amma babu mamaki wata ƙila idan ya bar madafun iko a yaba masa bayan ya sauka.

Sannan ya gargaɗi ƴan ƙasar da su kasance masu ɗa’a da bin dokokin ƙasa a yayin gudanr da babban zaɓen ƙasar na 2023 dake tafe nan da ƙasa da wata biyu tare da fatan samun ɗorewar zaman lafiya a ƙasar dama yankin Afrika baki ɗaya.

Da yake jawabin shiga sabuwar shekara Buhari yace gwamnatin sa ta yi aiki tuƙuru wajen kawo cigaba da kuma inganta rayuwar al’ummar ƙasar nan.

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *