VIDEO: “Budurwa ta kashe kanta saboda za ayi mata auren dole gobe a jihar Zamfara”

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Labarin da ke zo muna daga garin Magazu da ke cikin ƙaramar hukumar mulki ta Tsafe, jihar Zamfara Nijeriya wannan yarinya mai suna Hanifa mai kimanin shekaru goma shabakwai (17years) a duniya, ta hallaka kanta har lahira ta hanyar kwankwaɗar madarar fiya-fiya a sakamakon auren dole da iyayen wannan yariya suka tilasta mata.

A mahanga ta shari’a abin da wannan yariya tayi sam ba daidai bane, hasalima shiri’a ta tsawatar akan aikata wannan laifi, sai dai ita wannan yariya batada wani zaɓi wanda ya wuce wannan agare ta, domin kuwa a yanda labari yazo muna tayi duk abin da take iyayi don lurar da iyayen ta bata son wannan aure ya gudana amma duk da hakan uwayen wannan yariya sukai kunnen uwar shegu sai da sun kai son ransu.

Wannan yasa ita wannan yariya ta ɗauki wannan mataki na shan fiya-fiya wanda hakan ya zama silar rasa rayuwar ta, yin hakan ba daidai bane a musulunci amma muna nema mata afuwa da gafarar Ubangiji Allah Ta’alah ya gafarta mata ya kuma rahama mata.

Ina amfani da wannan dama domin ƙara kira ga uwayen yara musamman mata da su guji yiwa yariya auren dole, ayi ƙoƙari a baiwa yariya zaɓin ta matukar yanada siffofin da ake kallo wajen nema da bada aure.

Daga ƙarshe ina kira ga hukuma da tayi bincike na musamman don gurfanarwa da hukunta iyayen wannan yariya don ya zama izina ga mutanen baya.

Allah Ta’alah ya yafe mata Allah Ta’alah ya bamu lafiya zaman lafiya da kuma gamawa lafiya,.

saboda girman Ka ya Hayyu ya Kayyum🙏.

Views: 23

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *