Ta faru ta ƙare yau dai Hadiza Gabon ta bayyana kalar mijin da take son samu kafin tayi aure

Fitacciyar jarumar manaabtar shirya finafinan Hausa ta Kannywood Hadiza Aliyu Gabon ta bayyana cewa ita fa ba dole sai mai kuɗi zata aura ba, kawai jama’a na kallon kamar tana da dukiya shi yasa suke tsoron zuwa su aureta.

SIYASA

NNPP ta karyata jita-jitar sauyin sheka na Kwankwaso

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta karyata jita-jitar da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Hashimu Dungurawa, ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Kano.

Dungurawa ya ce Kwankwaso ba ya bukatar shawarar kowa wajen yanke shawarar siyasa, amma ya jaddada cewa babu wani shiri na sauya sheka.

“Ba mu da wata alaka da APC, kuma ba mu da niyyar sauya sheka,” in ji Dungurawa, yana karyata jita-jitar da cewa wani makirci ne kawai.

Ya nuna tabbaci cewa gwamnatin NNPP a Jihar Kano tana samun nasara kuma tana maido da doka da oda a yankin.

An rawaito shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano yana cewa kofar jam’iyyar a bude take ga Kwankwaso da sauran ’yan Najeriya da ke son sauya sheka.

Views: 6835

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *