Nifa tunda na daina soyayya shikenan na zauna lafiya har kyau jikina ya ƙara—Budurwa

Wata budurwa ta bayyana cewar tunda ta daina soyayya shikenan ta zauna lafiya jikinta har ya ƙara kyau a wani fafifan Bidiyon ta da jaridar Amintacciya ta wallafa

Shawara Daga TY Danjuma

Ƴan Nijeriya su kare kan su don gwamnati kaɗai ba za ta iya ba – TY Danjuma

Theophilus Danjuma, tsohon ministan tsaro, ya bukaci ƴan Najeriya da su dauki nauyin kare kan su a yanayin rashin tsaro da ke addabar ƙasar.

TheCable ta rawaito cewa da ya ke magana a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba, Danjuma ya ce abubuwan da suka faru na sace-sacen mutane da kuma hare-hare na baya-bayan nan sun kara nuna cewa ba za a iya dogaro da gwamnati kadai ba wajen kare ‘yan kasa.

“Na san muna da matsaloli da dama, ciki har da tsaro, kamar kwana biyu ko uku da suka wuce,” in ji shi.

“Mun fuskanci satar mutane kuka barazanar satar mutane za ta ci gaba da kasancewa har sai mun tashi tsaye mu kare kanmu.

“A bayyane ya ke cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya ba. Na yi gargadi tun da dadewa, a wani jawabi da na yi a Wukari, cewa dole ne mutanenmu su shirya don kare kansu.

“Wannan gargaɗin ya kasance kamar yau na yi shi.”

Views: 7230

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *