
Daya daga cikin dalibai ko almajiran Sheakh Malam Abduljabbar Nasiru Kabbara, ya fito karara ya yi ikirarin cewa, “Shi fa Malam Abduljabbar ko da a kan bata yake yana tare da shi kamar yadda ya bayya inda ya ce.
“Na yarda cewa Malam yayi kuskure amma dai wannan kuskuren ba zai sa in rabu da shi ko kuma in daina binsa a addinance da kuma koyi da dabi’unsa kyawawa ba.
Naji wasu daga cikin yan’uwa na barranta kansu da Malam saboda ya samu wata yar matsala, sun manta cewa Malam ya taka muhimmiyar rawa wajen tarbiyantar da su tare da dora su a kan hanya ma dai dai ciya.
Kuma wannan abin da suka yi ba shibe abinda addinin Musulunci ya horemu a kansa ba, idan kana son mutun don Allah to ko matsala ya samu bai kamata ka rabu da shi ba.
Kamata yayi ka kasance tare da shi da dadi ko babu dadi, saboda haka ni dai ina nan a kan bakana na kasancewa tare da malam har illa masha Allahu, kuma ko cikin bata yake tafiya ina tare da shi har lokacin da zai dawo kan dai dai domin ba’a yankewa mutum hukubci sai ya mutu.
In ji shi, mebebe ra’ayoyinku?
Views: 17
