
INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHIN RAJI’UN:
Ya Allah Muna Rokonka Da Kar Ka Sake Nunawa Al’ummar Musulmi Irin Wannan Mummunan Al’amari Maras Dadin Gani Ga Duk Wani Mai Imani:
Ku kalli Ka’aba dakin Allah yadda take a 2018 da yanzu 2021 lokacin Hajji

Lallai batun Corona Musulunci da musulmai kawai ake yaka ya Allah muna tawassili da girman wannan rana a wajenka, ya Allah muna kamun kafa da fiyayyen halitta mazonka mazon tsira ANNABI MUHAMMADU SAW ya Allah wadanna sarakuna masu iko da kasar Saudiyya .

Ba su suka bawa kansu wannan iko ba kaine ka lamunce kuma ka basu gashi ana hada baki da su wajen rusa addininka a doron kasa ya Allah ka sani sunyi wannan mummunan abu na hana aikin hajji wanda yana daya daga cikin rukkun addininka na Musulunci a shekarar data gabata sannan bana ma ga shi sun yi.

Ya Allah ka shiryi wadannan sarakuna na Saudiyya idan ba masu shiryuwa bane Allah ka kawar da su ka kawo wadanda za su bautawa addininka ameen.
Views: 108
