A karon farko shugaba Buhari yayi magana kan abinda ke faruwa da Abba Kyari

Rahotannin da muke samu daga birnin London na cewa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa dangane da abinda ke faruwa tsakanin FBI da shahararre kuma kwararren jami’in dan sandan nan wato Abba Kyari.

A cewar shgaban wannan abin takaici ne kwarai da gaske kuma za a tabbatar da cewa an yi sahihin bincike domin tabbatarwa ko kuma wanke wanda ake zargi.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin mai bashi shawara a kan harakokin da suka shafi yada labarai da sadarwa, tun a karshen makon daya gabata ne dai hukumar yan sandan Najeriya ta dakatar da jami’in dan sandan domin gudanar da bincike a kansa sakamakon zargin da FBI ke yi masa na karbar cin hanci da rashawa.

Views: 12

One thought on “A karon farko shugaba Buhari yayi magana kan abinda ke faruwa da Abba Kyari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *