
Tsohon Sarkin Kano, kuma kalifan darikar tijjaniya Malam Muhammadu Sanusi ya ce Allah ya yi masa baiwar da ba wani dan Najeriya da ya taki irin sa’ar da ya samu, Aminiya ta ruwaito.
A cewar tsohon Sarkin Sanusi wanda kuma shi ne Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wani taron gabatar da makaloli na shekara-shekara da aka gudanar kan cikarsa shekara 60 a duniya a ranar Asabar 14 ga watan Agusta.
A wani jawabinsa, Sarki Sanusi ya ce idan ya yi waiwaye ya dubi shekaru 60 da ya yi a duniya, yana shiga halin damuwa da kunci, saboda yadda aka samu koma-baya a bangarorin rayuwar yan Najeriya.
Views: 29
