
Rahotanni sun ce hukumar yaki da safarar mutane ta kasa, ta ce ta samu nasarar kama wani mai suna Emmanuel Stephen da laifin safarar budurwar shi mai shekaru 21 zuwa kasar Mali don ta yi karuwanci.
Jami’in hulda da jama’a na hukuumar, Vincent Adekoya, shine ya tabbatar da kama mutumin a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta ce mutumin dan asalin garin Akoko ne jihar Ondo, inda a yanzu yake zauune a Karmajiji, dake kan hanyar Aiport, a babban birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa, mutumin ya shafe shekara biyu yana soyayya da budurwar wacce take aiki a wani shagon kwalliya a Abuja.
A lokacin da ake bincike sanarwar ta ce, mutumin ya bayyana cewa yayarshi ce wacce take zaune a kasar Mali ta bukaci ya kai mata yarinya da za ta dinga yi mata aikin gida.
Sanarwar ta yi bayanin cewa mutumin ya shawo kan budurwar tashi akan tayi wannan tafiya mai hadari zuwa kasar Mali, tare da taimakon wani mai suna Trolley a Benin cikin jihar Edo, anyi safarar ta zuwa Mali a mota a watan Afrilu.
Ta ce duk da dai cewa saurayin ya sanar da budurwar cewa aikin gida kawai za ta yi a gidan ‘yar uwarshi, ya sayar da ita ga wata mata akan kudi naira miliyan daya da rabi (N1.5m), inda kuma aka tilasta ta zuwa karuwanci.
A yadda sanarwar ta nuna, cikin makonni kadan, sakamakon kwanciya da aka dinga tilasta ta tana yi da maza ya sanya ta dauki cuta da ta jefa ta cikin wani mawuyacin hali.
Ta ce duk da cewa yarinyar ta samu nasarar kiran iyayenta a Najeriya, matar taki amincewa ta kyaleta ta tafi, ta ce sai ta biya ta kudinta.
©Labarun Hausa
Views: 19
