Wani shararren malamin Islama a Najeriya ya sake yin batanci ga ANNABI SAW

Shahararren malamin addinin islamar nan na Najeriya mai suna Bello Yabo yayi wasu kalamai wadanda ke nuna cewa MANZON ALLAH SAW yana yin zagi idan ransa ya baci kamar yadda shima malamin addinin Islamar yayi.

A makon daya gabata ne aka rika yada muryar malamin inda yake dirkawa diyar kishiyar yarsa ashariya, dalilin da yasa ya bara a yammacin juya yana cewa manyan sahabban MANZON ALLAH SAW irin su Abubakar, Umar, Usman, Aliyu, suma suna yin zagi.

Har ANNABI SAW shina idan ransa ya baci yana yin zagi, in ji malamin wanda kuma yace yana da cikakkun hujjojin da ke tabbatar da hakan, kamar yadda ya bayyana a wani fai fan bidiyo wanda zamu kawo muku nan ba da dadewa ba.

Kalaman nasa dai sun soma tayar da kura inda mafi yawan jama’a ke ganin cewa eadannan kalamai na malamin kai tsaye cin mutunci da keta alfarma tare da yin batanci ga ANNABI SAW na.

Views: 29

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *