Dalilin da yasa na rushe kamfanin mai na NNPC—Buhari

A karshen makon daya gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayya cewa zai rushe kamfanin man kasar ko kuma ya rushe kamfanin man kasar na NNPC, wanda shugaban ya ce dalilin rushe kamfanin shine saboda a rage kudaden da ke salwanta a sakamakon cin hanci da rashawar da ya dabai baye kamfanin.

Sai dai a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar.

Fadar shugaban ƙasar tace rushe kamfanin na cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man fetur a Nijeriya karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.

Sai dai gwamnatin ta ce za a maye gurbin kamfanin na NNPC da wani mai zaman kansa.

Fadar shugaban ƙasar tace wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.

Ministan albarkatun man fetur Timipreye Silver ne zai jagoranci wannan kwamitin da zai lura da yadda za’a rusa kamfanin cikin nasara.

Zamu jira sharhin masana kan wannan yunkuri fage ne dake bukatar masana su fayyace shi. Dalla-dalla.

Masu karatu kuma kuna iya tofa albarkacin bakin ku.

Views: 41

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *