
A ranar Asabar dinnan ne limamin masallacin kasa dake Abuja Sheikh Ibrahim Makari ya shigar da karar Dr. Abdallah Gadanya, busa zarginsa da bata masa suna.
Sai dai wasu daga cikin mabiya sun soma yin kira ga Sheikh Dahiru Bauchi da ya takawa Makarin birki don kar a kara tada hankali tare da kawo rabon kawunan yan uwa musulmi.
Dambarwa ta barke Tsakanin Limamin Abuja Prof. Ibrahim Makari da Dr Abdallah kadon kaya.
Limamin masallacin Abuja Prof Ibrahim Makari ya garzaya kotun shari’a dake Jihar Kano kan abinda ya kira da yunkurin bata masa suna da wanda yake karar sa ya yi.
Prof Makari dai ya koka kan yadda Dr Abdallah ya yi ikirarin cewar suna da muryar sa lokacin da yake waya don bada kariya ga masu zagin Annabi Muhammadu S.A.W.
Lamarin da shi kuma Prof. din ya musanta tare da kalubalantar Dr. Abdallah Gadon kaya daya kawo muryar ko kuma ya nemi yafiyar sa a bainar jama’a, in ba haka ba su garzaya kotu.
Bayan rashin samun abinda ya nema Karara tare da cikan wa’adin da ya bashi ne Prof Makarin ya garzaya kotun don neman hakkinsa a gaban kotu.
Views: 64
