
INA MASU SHA’AWAR SHIGA AIKIN ‘YAN SANDA?
Ance waka a bakin mai ita tafi dadi, ga bayani cikin bidiyo daga bakin Maigirma shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria gwarzo mutumin kirki IGP Usman Alkali Baba akan batun diban sabbin ‘yan sanda
IGP Usman yace Maigirma shugaban Kasa Alhaji Muhammadu Buhari Maigaskiya ya bashi umarni ya debi sabbin ‘yan sanda dubu ashirin (20,000)
Idan baku manta ba, tun a shekarar 2019 hukumar kula da aikin ‘yan sanda Police Service Commission (PSC) ta shigar da karan ofishin shugaban ‘yan sanda IGP zuwa kotu akan batun diban ‘yan sandan, PSC tana cewa ita ke da alhakkin diba, IGP na cewa shi ke da alhakkin diba, akan haka sai kotu ta dakatar
Shine yanzu shugaba Buhari yayi watsi da bukatar PSC ya bawa IGP umarni ya debi sabbin ‘yan sandan har da na shekaran da ta gabata 2020 da ba’a deba ba, za’a hada da wannan shekara a debi dubu 20
Don haka duk wanda yake da bukatar shiga aikin ‘yan sanda ya kasance cikin shiri, wanda yake da matsala na takarda ya gyara, wanda shekarunsa sun wuce 25 shima ya gyara, sannan ayi hankali da ‘yan damfara, duk wanda yace ka kawo kudi zai sama maka aikin ‘dan sanda a yanzu to madamfari ne kowaye
Ku kasance da shafin Datti Assalafiy, da zaran rundinar ‘yan sanda ta fitar da bayani akan hanyoyi da ka’idoji na diban ‘yan sandan zan sanar daku Insha Allah
Allah Ya bawa mai rabo sa’a Amin.
KARIN LABARAI:
Views: 13
