
Tun bayan haduwar Kwankwaso da Ganduje a filin jirgi wasu daga cikin yan kwankwasiyya ke bayyana cewa ai haduwar barawo da mainkaya aka yi duk da cewa basu bayyana ko waye barawon a cikinsu ba.
Amma a jiya ne sashin Hausa na BBC ya yi fira da tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa kwankwaso, ga rahon BBC game da firar.
Kwankwason ya bayyana haka ne a wata doguwar hira da ya yi da BBC inda ya taɓo abubuwa da dama musamman waɗanda suka shafi siyasar Najeriya.
Baya ga batun fansho, tsohon gwamnan ya ce shi ne kaɗai wanda ya yi gwamna a jihar da gwamnati ba ta siya mashi gida ko ofis ba.
Sai dai Sanata Kwankwaso ya ce da alama saboda yana ɓangaren masu adawa ne shi ya sa ake masa haka.
“Idan da tare nake da su, da haƙƙina dole za a biya ni, albashina da za ku bani ko fansho duk wata wanda kowa ake ba shi, ni ba a bani, na kuma yarda saboda ina ɓangaren adawa a je a ci daɗi lafiya,” in ji Sanata Kwankwaso.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa a farkon shekarar 2021, an shaida masa cewa an kai sunayen mutum tara gaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ciki har da sunansa inda ya zargi cewa an yi haka ne domin a zubar musu da mutunci.
Amma kuma ya bayyana cewa ko yanzu EFCC din ta aika masa da goron gayyata zai karɓa, inda ya ce “Ko yanzu na gode wa Allah, shekarata 30 cikin wannan harka babu wani wanda ya taɓa zuwa ya ce naira biyar ɗinsa ta ɓata, idan ma ka zo ka ce mani naira biyar ɗinka ta ɓata, nima zan so na ga wanda ya ɗaukar maka naira biyar”.
Duk a cikin hirar da ya yi da BBC, Sanata Kwankwaso ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda al’amuran tsaro ke tafiya a Najeriya.
Ya ce yana mamaki kan irin abubuwan da gwamnati ke faɗa game da tsaro da kuma irin sakamakon da ake samu.
“Wasu jihohi ma musamman a Katsina, waɗanda suke kan iyaka kamar irin su Jibiya sai ka ji mutane ana hira da su a manya-manyan gidajen rediyo na duniya har ma suna cewa su yanzu suna kira ga sojojin Nijar su taimaka musu.”
Sanata Kwankwason ya kuma ce ya yi minista na tsaro a Najeriya kuma ya san yadda abubuwa suke shi yasa yake mamaki kan irin abubuwan da ke faru.
KARIN LABARAI:
Views: 7
