A karshen makon daya gabata ne aka shawarci Majalissar dattawan Najeriya a kan ta canzawa Najeriya suna daga Federal Republic of Nigeria, zu United Africa Republic, sai dai wasu na ganin cewa wannan suna bai dace da kasar ba.
Yayin da a bangare guda wasu daga cikin yan kasar ke bayyana cewa suna goyon bayan sanza sunan daga Najeriya zuwa Jamhuriyar hadin kan kasashen Afrika, saboda sunan ya dace da ita kasancewarta uwa kuma jaga a fannin yawan al’umma da kuma karfin tattalin arziki.
Ku menene ra’ayoyinku, dangane da wannan batu? Shin kuna goyon bayan a canzawa kasar suna ko kuma a barta a Najeriyar ta?
Views: 26
