Ra’ayoyin yan Najeriya dangane da dakatar da Twitter a kasar

A ranar juma’ar data gabata ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin sadarwar Twitter a kasar saboda wasu dalilai, ga ra’ayoyin wasu yan Najeriya dangane da wannan mataki.

Ibrahim Sani: ina goyon bayan dakaymtar da Twitter, saboda sun raina gwamnatin Najeriya

Sagir Musa: Ina maraba da wannan mataki da gwamnati ta dauka a kan Twitter, domin ba shi da wani amfani ga kasar mu

Ummusalma Yusuf: Bana goyon baya saboda wasu ta nan suke samun abincinsu kuma rufewar zai iya shafar kasuwancinsu

Sanata Bukola Saraki: Ina kira ga gwamnatin Najeriya da ta sake duba batun dakatar da Twitter domin hakan ya sabawa dokokin Dimokuradiyya

Anas: Bayna goyon bayan dakatar da Twitter

Hukuncin da Gwamnatin taraiya ta dauka na dakatar da dandalin sada zumunta na twitter hukunci ne tsatstsaura kuma wanda zai wa gwamnatin illa a idan duniya idan akai laakari da maganar tauye hakkin dan adam da yancin sa.

Akwai abubuwan dubawa a matakin na Gwamnatin taraiya kamar haka;

Na farko dai baza su iya hana mutane hawa twitter ba, yanzu ma kafin nai wannan post din a nan shafi na na Facebook na bar mutane da dama suna amfanin da twitter. Tabbas masu amfani da ita zasu ragu, kafin mutane su gane yadda zasu dinga hawa ta wasu yan dabaru da ake yi. Sannan yan Najeriya da basa kasar suma tsaf za suyi amfani da ita ba wani tsaiko.

Magana ta biyu, shi ne akwa yan kasuwa da dama da suke amfani da shafin twitter domin tallata hajar su, kuma ta haka suke samun kudin shiga, domin rike kan su da iyalan su. Dakatar da shafin twitter zai shafi cinikaiyar su domin saboda wannan hukunci na Gwamnatin taraiya.

Hujjar da gwamnatin taraiya ta bayar na dalilin ta na rufe shafin twitter shine maganar cewa twitter ta na bada dama wajen wargatsa Najeriya, duk da akwai kanshin gaskiya a cikin wannan maganar, toh amma abin dubawa a nan shine gwamnatin taraiya tana ina kafafan yada labarai na kasar nan, musamman jaridun Kudu, wanda suke karkashin hukumomin sa ido kamar NBC da makamantan su, wanda a kullum suke saka labarai na bogi, da na tunzura al’umma da makamantan su, wanda ko sau daya Gwamnatin bata taba daukar wani mataki akan su ba? Ka saurari shirye shiryen gidajen radio musamman na siyasa, ka ji yadda ake keta haddin dan adam da kazafi, da cin zarafi, wanda duk sun karya doka, amma har gobe gwamnati ta ki daukar mataki akan su, saboda mafi yawanci su yan gwamnatin ke turo mutane su ci mutuncin abokan adawar su. Kaga kenan a wannan batu gwamnati kukan karya take domin kuwa, kamata yayi ta duba duk wadannan abubuwa da na zaiyana a sama, idan dai da gaske take.

Ya zama wajibi gwamnatin taraiya ta kare hakkin yan kasa akan basu daman fadar yancin bakin su bisa ka’ida a koyaushe, wannan kundun tsarin mulkin Najeriya ya ba mu wannnan damar, haka kuma ya zama wajibi gwamnati ta hukunta duk wanda ya keta doka, ya wuce gona da iri domin shi yasa ake da hukuma. Ba daidai bane ace saboda gazawar gwamnati wajen hukunta masu keta ka’ida, ace kuma gwamnatin ta keta namu hakkin na yancin mu. Wannan, babban kuskure ne.

Saboda haka ni ba na goyon bayan wannan matsayi na gwamnatin taraiya, idan yau twitter aka rufe, gobe Facebook kenan zaa rufe, jibi kuma sake rufe wani, kuma bacin gazawar gwamnatin ne ya ja har ake samun wuce gona da iri, da ake yi wajen amfani da kafofin sada zumunta na zamani.

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *