Mun sa a tsaurara bincike duk wanda aka gani yana amfani da Twitter, a kama shi—Buhari

Fadar mulki ta Abuja ta gargadi yan Najeriya, da su shafawa kansu lafiya su daina amfani da shafin Twitter, subi doka da order idan kuma ba haka ba duk wanda aka kama yana amfani da shafin zai fuskanci hukunci saboda haka muna gargadi zuwa ga masu taurin kunne da su bi doka.

Idan ba’a manta ba a yammacin ranar jiya Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da kamfanin na Twitter gaba daya a fadin kasar wanda hakan ya jawo zazzafar muhawara da cecekuce a ciki da wajen kasar, dalilin da har ya jawo wasu daga cikin al’ummar kasar suka soma amfani ta haramtacciyar hanya wajen amfani da shafin.

Wasu daga cikin yan kasar dai sun karkata wajen amfani da kafar sadarwar WIFI ko VPN wajem amfani da shafin dalilin da ya sa gwamnatin kasar ta ce za’a hukunta duk wanda aka kama yana amfani da shafin ta wannan haramtacciyar hanya.

Menen ra’ayinku?

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *