
Shugaba Buhari Ne Zai Yanke Makomar DCP Abba kyari, Cewar Ministan Lamurran ‘yan Sanda Muhammadu Maigari Dingyadi
Daga Abubakar A Adam Babankyauta.
Ministan Lamurran ‘yan Sandan Nijeriya Muhammadu Maigari Dingyadi yace Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne zai yanke matsaya ta karshe kan matakin da za’a dauka a kan DCP Abba Kyari, da wata kotun kasar Amurka ta bukaci a kamo mata shi, bisa tuhumarsa da alaka da Hushpuppi.
Ministan Lamurran ‘Yan sandan Nijeriya Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ne zai yi matsaya ta karshe dangane da lamarin DCP Abba Kyari, tsohon shugaban runduna ta musamman ta yaki da aikata miyagun laifuka ta ‘yan sanda.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels, TV Dingyadi ya ce gwamnatin Nijeriya na bukatar ganin an yi duk abin da ya kamata akan lamarin Abba Kyari, kasancewar yana da alaka da matakin kasa-da-kasa.
Ministan Lamurran ‘yan Sanda Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce kamar yadda kowa ya sani ne rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kafa wani kwamiti domin yin cikakken bincike akan dukkan zarge-zargen da ake yi wa DCP Abba Kyari, kuma tuni kwamitin ya kammala aikinsa tare da mika rahotonsa ga babban Sufeto Janar na ‘yan sanda.
Ministan ya ce haka kuma an gabatar da rahoton kwamitin da shawarwarin da ya bayar ga ministan shari’a na kasa domin jin ra’ayinsa, a yayin da kuma ita ma ma’aikatar harkokin kasashen waje, za’a gabatar mata da rahoton, kafin daukar mataki na karshe akan lamarin.
“Abin da ya kamata ‘yan Nijeriya su sani shi ne, hukumomin ‘yan sanda sun yi na su aiki kamar yadda ya kamata, kuma a bayyane suka gudanar da komai. Abin da ya rage yanzu shi ne shugaba Muhammadu Buhari ne zai yanke shawarar matakin da za’a dauka akan lamarin,” in ji Maigari Dingyadi.
Views: 74

Allah yakyauta
Allah yasa aywa abba kyari adalchi
Allah ya kyauta wanna sai kasata Nigeria