Sojan da ya jagoranci juyin mulki a Guinea ya sha rantsuwar kama aiki

An Rantsar Da Sojan Da ya Jagoranci Juyin Mulki A kasar Guinea

Sabon shugaban kasar Guinea dan shekaru 41 da haihuwa Mamadi Dambouya da ya jagorancin kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Alpha konde ya sha rantsuwar kama aiki ne a jiya juma’a a babban dakin taro na Mohammad na 4 d ake birnin Konakry , bukin rantsuwar da mafi yawancin shuwagabannin Afrika suka kaurace ma.

Tun a watan da ya gabata ne kungiyar tarayyar Afrika da Ecowas suka kakabawa kasar takunkumin karyar tattalin arziki, da ma wasu daga cikin wadanda ke da hannu wajen juyin mulkin da danginsu, da kuma rike dukiyoyin da suka mallaka a kasahen waje da kuma hana su yin tafiye tafiye zuwa kasashen ketare.

Yanzu haka dai kasashen yankin na fatan ganin gwamnatin rikon kwarya da sojoji suka kafa ta zama ba ta da tsawo da kuma gaggauta mika mulki ga hannun farar hula domin komawa turbar demukuradiya.

Ana san bangaren sabon shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mamadi Donboya ya yi alkwarin kawo sauye –sauye a tsarin mulkin kasar da kuma sake fasalin dokokin zabe da kundin tsarin mulkin da kuma yaki da cin hanci da rashawa da ya ta’azzara a kasar.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *