
Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya na fama da rikicin cikin gida wanda yaƙi ci yaƙi cinyewa.
Inda har wasu daga cikin masu adawa da jam’iyyar suka soma yin rubuta ce rubuce a kan wannan rikici.
Zazzafan rikici da rabuwar kai ya barke a cikin jam’iyyar PDP a dalilin fitar da dan takaran shugaban kasa.
Shugabannin jam’iyyar da suka fito daga kudancin Nigeria sunce dole ne wanda zai tsaya takaran shugaban kasa a PDP ya fito daga kudancin Nigeria kuma wanda ba Musulmi ba.
Sai dai wannan batu ya tashi hankalin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka fito daga yankin Arewa, sunce sam ba zasu yadda ba, a halin yanzu suna cacar baki wanda alama ke nuni da rugujewar jam’iyyar.
Kwanakin baya VOA tayi hira da Buba Galadima yace har yanzu dai halin rashin gaskiya da aka san PDP da shi yana nan babu abinda ya canza, wanda hakan ke nuni da cewa shima ya fice daga jam’iyyar.
Shi kuma tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya zargi shugabannin PDP na kudancin Nigeria da son rai, inda yace sam ba zasu amince da bukatar su ba na fitar da dan takaran shugaban kasa daga kudu, ku ziyarci BBC Hausa ku karanta abinda Sule Lamido yace.
Wannan rikicin na PDP zai taimaki APC, duk da itama APC din tana fama da nata rikicin akan batun fitar da dan takaran shugaban kasa tun kafin barazanan da Gwamnonin kudancin Nigeria sukayi na cewa muddin ana son Nigeria ta tabbata a matsayin kasa guda, to dole wanda zai maye gurbin shugaba Buhari ya fito daga kudu.
Muna fatan Allah Ya bamu shugaba na kwarai.
Daga Datti.
Views: 5
