
Gwamnatin Najeriya ta ce gwamnoni sun gane kuskurensu na yin sulhu da ƴan fashin daji masu satar mutane a jihohin arewa maso yammacin ƙasar.
Ministan yada labaran kasar, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wani shirin safe (Good Morning Nigeria) na kafar talabijin ɗin ƙasar NTA na ranar Talata.
Ministan ya ce gwamnoni ba su gane cewa bai kamata su yi sulhu da ƴan bindiga ba, inda yanzu suka fahimci kuskurensu.
“Gwamnonin sun koyi darasi daga kura-kuran da suka faru a baya kuma sun yanke shawarar cewa ba za su tattauna da ‘yan fashi ba sai dai su fatattake su,” in ji ministan.
Ya ƙara da cewa yanzu ne gwamnonin suka ɗauki matakan da suka dace na magance matsalar ƴan bindigar.
A cewar Lai Mohammed, matakan katse hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwannin mako da hana sayar da baburan da sayar da man fetur suna aiki a yanzu.
Ya ce an toshe hanyoyi da dama da ke da alaƙa da ƴan bindigar, musamman katse hanyoyi na mu’amularsu ta samun bayanai da abinci.
Sai dai ministan yaɗa labaran na Najeriya wanda ya ce matsalar ƴan fashin daji matsala ce da ta shafe tsawon shekaru 10 a Najeriya, ya ce halin da matsalar ta jefa ƙasar ba batu ba ne na yanzu.
Lai Mohammed ya ɗora laifin ruruwar matsalar ga rashin shugabanci nagari.
Amma ya yaba wa gwamnonin yankin arewa maso yammaci waɗanda ya ce yanzu sun haɗa kansu domin tunkarar matsalar.
Views: 15
