Duk wanda ba ya son Maulidi ba musulmi bane—Sheikh Maƙari

A wata sabuwar hira da ya sake yi da tashar can ta Kasar Ghana mai suna Alpha Radio, Prof. Maqari a kokarinsa na halasta Maulidi ya sake fadin cewa; Maulidi shi ne “Murnan samuwar Annabi (saw)”, sai kuma ya yi ishara da cewa; wannar ma’ana ta Lugha ce. Alhali a matsayinsa na kwararre a Harshen Larabci bai ambato mana shawahid daga wakoki da maganganun Larabawa a kan wannar ma’ana ba.

Don haka wannan ba karbabbe ba ne a tsari na Ilimi.

Na biyu: Sai kuma ya kafa hujja a kan bikin Maulidin, da abubuwan da suke yi a cikinsa da wata ka’ida kamar haka:
((الإباحة الأصلية))

To a nan mu abin da muke so mu sani, shin su Prof. Maqari suna daukar Maulidi ne a matsayin Ibada ko Mu’amala?
Idan Maulidi a babin Mu’amala yake, wato “Mubahaat” to a nan zai kafa hujja da wannar ka’ida. Sai Maulidin ya zama dadai yake da bikin murnan ranar samun ‘yancin Nigeria daga mulkin mallaka.

Amma idan kuma Maulidi a babin Ibada yake, da neman kusaci zuwa ga Allah to sai mu ce: wa ya muku izni da yinsa?
Saboda abubuwa na Addini da Ibada ba a yi sai da Izni daga mai shar’anta Shari’a. Allah ya fadi a Ayar da yake munzanta Mushrikai a cikinta ya ce:
{أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُمْ مِنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَنْ بِهِ اللَّهُ} [الشورى: 21]

{Ko suna da ababen shirka ma Allah ne suka shar’anta musu a Addini abin da Allah bai yi izni da shi ba?}.

Ashe abu ba ya zama shar’antacce a Addini sai Allah ya yi izni da shi, ta hanyar Wahayi a Alkur’ani ko ta harshen Manzonsa (saw).

Don haka a ina Allah ya yi muku izni da yin Maulidi?!

Haka Hadisi ya zo Annabi (saw) ya ce:
«من أحدث في أمرنا هذا ما ليس فيه، فهو رد»
صحيح البخاري (3/ 184) صحيح مسلم (3/ 1343)

((Duk wanda ya kirkiri abin da ba ya cikin wannan lamari namu (na Addini) to abin mayarwa ne)).

A riwayar Muslim:
«من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد»
صحيح مسلم (3/ 1343)

((Duk wanda ya yi wani aikin da babu umurninmu a kansa to abin mayarwa ne)).

To ka ga idan dai Maulidi Addini ne, to muna bukatar ku kawo mana inda Annabi (saw) ya yi umurni da aikata shi, idan kuma ya zama an kira shi da sunan Addini, amma babu izni da umurni daga Allah to lallai abin mayarwa ne, ba ya cikin Addini, ko da casa’in bisa dari (90%) na Musulmin Duniya ne suke aikatawa.

Na uku: Sai kuma ya ambaci wata ka’ida a babin Qiyasi, cewa; dukkan ibada da aka san “illa” na shar’anta ta to za a iya yin Qiyasi a kanta. -Wai- sai suke yin Qiyasin Maulidi a kan Azumin Ranar Litinin.

A can baya na taba yin rubutu na yi raddin wannar shubuhar tasa. Amma a takaice; wannan bataccen Qiyasi ne, saboda ba a bukatar wani karin Ibada bayan ga nan Azumi da Annabi (saw) yake yi a munasabar haifuwar a duk sati, a ranar Litinin.

Na hudu: Sai kuma ya yi kokarin hana mu yi musu inkari, yana mai kafa hujja da wata ka’ida, don ya nuna kowa yana da daman ya yi Maulidinsa yadda ransa yake so, ya ce:
((لا إنكار في مسائل الخلاف))

Alhali yin amfani da wannar ka’idar a sake ba daidai ba ne, saboda Malamai sun kayyade ta da mas’alolin da babu Nassi ko Ijma’i ko ingantaccen Qiyasi a kansu. Amma mas’alolin da aka samu Nassi ko Ijma’i a kansu, to wanda ya saba musu dole a yi masa inkari. Shi ya sa Imam Nawawiy ya hakaito daga Malamai ya ce:
((قالوا ليس للمفتي ولا للقاضي أن يعترض على من خالفه إذا لم يخالف نصا أو اجماعا أوقياسا جليا))
شرح النووي على مسلم (2/ 24)

((Malamai sun ce: Mai Fatawa ko Alkali ba shi da daman kalu-balantar wanda ya saba masa idan bai saba Nassi ko Ijma’i ko Bayyanannen Qiyasi ba)).

Ashe idan mutum ya saba dayan ukun nan, Nassi ko Ijma’i ko Bayyanannen Qiyasi to dole za a yi masa inkari.

Kuma irin wannan kafa hujja da Prof. Maqari yake yi, cewa; kar a yi musu inkari a kan Maulidi, saboda an yi sabani, su sun saba ma Ahlus Sunna, su fahimtarsu ita ce a yi Maulidi, tun tuni Imam al-Shadibiy ya koka a kan irin wannar mummunan dabi’a da take da hasari a Addini, inda ya ce:
((وقد زاد هذا الأمر على قدر الكفاية؛ حتى صار الخلاف في المسائل معدودا في حجج الإباحة، ووقع فيما تقدم وتأخر من الزمان الاعتماد في جواز الفعل على كونه مختلفا فيه بين أهل العلم، لا بمعنى مراعاة الخلاف؛ فإن له نظرا آخر، بل في غير ذلك، فربما وقع الإفتاء في المسألة بالمنع؛ فيقال: لم تمنع والمسألة مختلف فيها، فيجعل الخلاف حجة في الجواز لمجرد كونها مختلفا فيها، لا لدليل يدل على صحة مذهب الجواز، ولا لتقليد من هو أولى بالتقليد من القائل بالمنع، وهو عين الخطأ على الشريعة حيث جعل ما ليس بمعتمد متعمدا وما ليس بحجة حجة)).
الموافقات (5/ 92 – 93)

((Hakika wannan lamari ya wuce kima, har ya kai ga wasu suna kirga sabani a kan mas’ala cikin dalilai a kan halascinta…
Sau da dama za a yi Fatawa a kan abu, a ce: bai halasta ba, sai a ce ma wanda ya ba da Fatawar; me ya sa ka ce: bai halasta ba, alhali an yi sabani a kan mas’alar? Kawai sai ya sanya yin sabani a kan mas’alar shi ne hujja a kan halasci, don kawai mas’alar ta kasance an yi sabani a kanta, ba don saboda akwai dalili na Shari’a da yake nuni a kan ingancin ra’ayin halascin ba, ba kuma saboda yin taklidanci ga wanda ya fi cancanta da taklidancin a kan wanda ya ba da fatawa da rashin halascin ba. Wannan shi ne ainihin kuskure ma Shari’a, ta yadda aka sanya abin da ba a dogaro a kansa a matsayin abin dogaro, aka sanya abin da ba hujja ba a matsayin hujja)).

Don haka kasancewar an yi sabani a kan mas’ala ba hujja ne na kasancewarta halas ce ta zama Addini ba, saboda Addini dole sai da izni da umurni daga Allah. Ba a shisshigi ma Allah a lamarin Addini.

Saboda haka Malamai suka ce: Sigar ka’idar ga yadda ya kamata ta kasance:
((لا إنكار في مسائل الاجتهاد.))
التحقيق والبيان في شرح البرهان في أصول الفقه (3/ 282) الفوائد الجسام على قواعد ابن عبد السلام (ص: 354)

((Babu inkari a mas’alolin Ijtihadi)).

Ma’ana; mas’alolin da babu Nassi karara a kansu, ko Ijma’i ko Bayyanannen Qiyasi, sai aka yi Ijtihadi a kansu to ba a inkari a kansu. Saboda ba a warware Ijtihadi da Ijtihadi.

Saboda haka wannar ka’idar ba hujja ba ce ga Prof. da ‘yan Mazhabarsa.

Na biyar: Sai kuma Prof. Maqari ya yi ishara ga Malaman da suka yi magana a kan Maulidi, irin su Ibnul Hajj da sauransu, alhali wadannan Malamai an san abubuwan da suka fada na inkarin Maulidi.

A takaice, a bisa hakika duk abubuwan da Prof. Maqari ya fada ba su da kima a ilmance.

Allah ya shiryar da su, ya sa su gane, mu kuma ya kubutar da mu, ya kiyaye mu.

✍️Aliyu Muh’d Sani

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *