APC ta nemi INEC ta soke zaɓen jihar Anambra

A Gaggauta Soke Zaben Anambra, ~ Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Anambra

Muna so a gaggauta soke zaɓen Anambra – cewar Chief Basil Ejidike Shugaban jam’iyyar APC na jihar Anambra.

Abin da ke faruwa a Anambra ba zaɓe ba ne illa babban maguɗin zaɓe ne, kuma muna son duniya ta ji muryarmu cewa ba za mu taɓa amincewa da sakamakon zaɓen Anambra ba.

Dan takarar jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) da kuma Gwamna mai ci Willie Obiano sun yi amfani da tsarin zaɓe gaba ɗaya, kuma za mu tsaya tsayin daka wajen hana shi.

Ndi Anambra yana son Gwamna APC kuma babu wani abu da wani zai iya yi don hana su wannan dama, kusan mun samu nasara a dukkan ƙananan hukumomin amma Willie Obiano da Charles Soludo ta hanyar cin hanci da rashawa jami’an INEC sun murguɗa duk wani tsari na jam’iyyar APGA.

Muna son INEC ta soke zaɓen, ta kuma sanya ranar da za a sake gudanar da sabon zaɓe ba tare da maguɗi ba amma idan INEC ta ci gaba da bayyana sakamakon zaɓe,.

To ko shakka babu za mu ƙalubalanci yadda zaɓen ya gudana a kotun shari’a, har zuwa kotun ƙoli. Babu wanda zai iya ba mu tsoro.

Daga Baba Abdullahi.

Views: 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *