
A ƙarshen makon daya gabata ne gwamnatin jihar Katsina ta ce tana sake duba yanayin da halin tsaro ke ciki a ƙananan hukumomi 13 waɗanda aka rufe musu sabis sanadiyyar rashin tsaro.
Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar da ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa, yanzu haka mai girma gwamnan jihar ta Katsina Hon. Aminu Bello Masari.
Ya karbi rahoto tsaron jihar kuma yana cigaba da duba wa tare da yin nazari, don yanke hukunci, ana sa rana gwamna Masari, zai bada umarnin bude layukan sadarwa a wasu daga cikin ƙananan hukumomi 13 da aka rufe.
Majiyar ta ƙara da cewa mawuyaci ne a buɗe illahirin ƙananan hukumomin da abin ya shafa amma ana sa rana za’a buɗe biyar daga cikinsu da suka haɗa da.
- Malumfashi
- Funtua
- Bakori
- Ƙafur
- Ɗanja
Views: 16
