Masana sun tabbatar da cewa wannan shine gidan ANNABI MUHAMMAD SAW

Shafin Fityanu ya wallafa hoton da aka yi amanna cewa gidan ANNABI MUHAMMAD SAW ne.

Masana tarihi sun tabbatar da cewa wannan gida shine inda Annabi Muhammadu ﷺ yayi rayuwa a cikin sa.

“Yan’uwa ku dubi yadda gidan Manzonmu ﷺ yake wanda aka ba shi dukkan abin da ke cikin sammai da ƙasa duk da haka ya rayu cikin sauƙi.

Sayyida A’isha ta ce watanni za su shude kuma Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallama ba shi da abin da zai ci a gidansa sai dabino da ruwa Bai taba cin abinci ba duk tsawon rayuwarsa a Madina.

Yakan daure duwatsu a cikinsa yana kwana a kan tabarma ya bar tabo a bayansa kuma da ganin haka sai sahabbai suka yi kuka – duk da haka shi ne ya fi kowa godiya kuma baya barci da daddare ba, sai dai ya raba wa mabukata abunda yake hannunsa.

Allah ya bamu da yawa duk da haka muna tunanin ba mu da komai, Muna da firij da akwatunan da suka cika duk da haka har yanzu ba mu gamsu ba, Muna da dakuna masu daɗi amma har yanzu zukatanmu suna jin tashin hankali, Kuma muna samun abinci a faranti sau 3 a rana, duk da haka har yanzu muna jin babu koshi ba.

Allah ya kara yarda dashi, ya kara mana soyayyan sa duniya da lahira. Amin.

©Fityanumedia

Views: 38

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *