
Dan Najeriyan Da Ya Aura Ba’maurkiya Ya Dawo Da Ita Najeriya Da Zama

Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel
“Wani matashi mai suna Itakpe dan asalin kabilan Ibo da aka Haifa a Najeriya, da ya auri Y’ar Kasar Amurka. ya dawo da ita Kasar Sa wato Najeriya A Domin su cigaba da rayuwar Su A Kauyen Su dake Jihar Imo, dan koba komai baturiyar ta kara shakuwa da Y’an uwan sa.”
“An iya hango ba’amurkiyan da mijin na ta, a wurin burtsatsai ta famfo don a nuna mata inda ake debo ruwa, kana kuma ya turata gona tare da Y’ar uwan sa mai suna Isoma domin a nuna mata yadda za ta yi aikin gona dai-dai gwargwado iyawar ta.”
“Majiyar mu mai tsuhe Daga makusancin mijin baturiyan, ya cigaba da ce wa, da amincewar matar ta sa ne suka dawo Najeriya da zama, domin su cigaba da rayuwar su a inda aka haifi mijin ta.”
Sai dai kuma a takardan yarjejeniyar da aka rubuta ta dawowar baturiyar Kasar da aka haifi mijin na ta Najeriya, takardan yana dauke da ce wa, wani bayan lokacin dazaran baturiyar itama ta bukaci ganin gida zuwa Amurka Zara shilla Amurka din domin ta gano Y’an uwan ta.”
Views: 9
