Yadda jami’an hukumar kiyaye haɗurra ke takurawa al’umma a jihar Kebbi

Kiraga Hukumar Kiyaye Haɗarurruka Ta Jihar Kebbi Data Ƙasa Dasu Ɗauki Matakin Daya Dace Bisa Rashin Ɗa’a Da Rashin Sanin Makamar Aiki Da Yan’uwansu Suka Aikata Na Ƙaramar Hukumar Mulki Ta Argungu.

Daga: Abdulmajid Abdullahi

Ma’aikatan kiyaye Haɗarurruka ta karamar hukumar mulki ta Argungu, sunyi rakiyar wani yaro kamfen batare da rakiyar jami’an yan-sanda ba kokuma civil defence cikin garin Argungu.

Tambaya ana shine kundin tsarin mulki na ƙasa yabasu damar aikata haka, kokuma sunyine domin rashin sanin makamar aiki, kokuma sun aikata hakane domin biyan tasu buƙata?

Sunabi cikin anguwa suna tada ma al’umma hankali wani abun ban hausi hadda jiniya tamkar sun dauko majinyaci wanda yake neman agajin gaggawa.

Al’ummar gari suna jiran hukuma tayi aikinta akansu kokuma mutanen gari su dauki matakin daya dace akan wannan rashin ɗa’a da rashin sanin makamar aiki irin na jami’an kiyaye haɗarurruka suka aikata wannan babban laifine.

Rahoton Abdulmajid Abdullahi

Phone Number: +234 701 140 4295

Views: 33

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *