Dalilin da ya sa na fita daga cikin shirin labarina—Nafeesat Abdullahi

“Ba Zan Ƙara Fitowa A Cikin Shirin Fim Ɗin Labarina Ba”. Cewar Jaruma Nafisa Abdullah.

Ƙwararriyar Jarumar Nafisa Abdullahi Ta Rubuta Takardar Janyewa Daga Cigaba Da Fitowa A Shirin Mai Dogan Zango Na Labarina, Sakamakon Hidimomin Kashin Kanta Da Suka Yi Mata Yawa.

Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Janyewa Daga Cigaba Da Daukar Shirin, Wanda Ta Aikewa Malam Aminu Saira, Wanda Jaridar Blueink News Hausa Ta Samu Kofin Wasikar Wadda Jarumar Fina-finan Kannywood Nafisah Abdullahi Ta Sanyawa Hannu Mai Dauke Da Kwanan Wata 1/1/2022.

A Cikin Wasikar Ta Ci Gaba Da Cewa “Na Fita Daga Cikin Shirin Ne Saboda Yadda Al’amurra Suka Yi Min Yawa, Da Hakan Na Tabbatar Ba Zai Bani Damar Ci Gaba Da Fitowa A Shirin Mai Dogan Zangon Ba.

Ta Ce “Na Ji Dadin Kasance Wa Cikin Shirin Labarina Kwarai Da Gaske, Kuma Na Yi Mu’amala Mai Kyau Da Dukkanin Abokanan Aikin Na Cikin Shirin, Tun Daga Kan mai Shirya Shirin Har Zuwa Sauran Abokan Aiki.

Daga Karshe Jarumar Ta Ce “Ina Son In Maida Hankali Kan Kasuwancina Da Kuma Amfani Da Kamfanina Harma Da Shirin Fim Da Nake Yi Na Kashin Kaina”. Injita

Views: 48

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *