
Rahoton sashin Hausa na BBC ya bayyana cewa Sheikh Ibrahim Elzakzaky ya ce yana fatan wata rana zai dawo Zariya.
Sheikh Ibrahim Elzakzaky ya bayyana hakan ne a hirarsa ta farko da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta Hausa tun bayan da aka sako shi.
Fiye da shekara shida kenan tun bayan rikici tsakanin mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojoji suka yi na cewa mabiya El-Zakzaki sun tare musu hanya a Zaria.
Ɓangaren Sheikh Zakzakin dai ya sha musanta batun tare hanyar inda suke cewa gwamnati ta yi amfani da hakan ne domin far musu a 2015.
Ƙungiyar Amnesty International ta ce wutar da sojoji suka buɗe kan mabiyan Zakzaky ta yi sanadin mutuwar mutum 345 a lokacin.
A watan Yulin 2021 kuma, wata babbar kotu a Kaduna ta wanke Sheikh Zakzaky da mai ɗakinsa daga dukkan tuhume-tuhumen da aka yi musu inda kuma aka sake shi bayan kwashe kimanin shekara shida a tsare.
Views: 16
