2023: Gen Election “Kotu ta ɗaure mutumin da da INEC ta kama da katin zaɓe sama da 100”

Suprime Court Abuja

Ana wata ga wata a jiya ne muka samu labarin cewa.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta bada sanarwar samun nasarar gurfanar da Nasir Idris a kotu, kuma har an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a kurkuku.

An ɗaure Nasir ne bayan an kama shi da katin zaɓe har 101 A hannun sa.

A wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ya fitar, ya ce an yanke wa Nasir hukunci a Kotun Majistare ta Sokoto.

Jami’an ƴan Sandan Jihar Sokoto ne su ka kama shi a ranar 10 ga Oktoba, aka same shi da tulin katin zaɓe har 101, a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Jihar Sokoto,” inji Mr Okoye.

Bayan ‘yan sanda sun kammala binciken su, sun aiko mana da fayil ɗin da ke tattare da bayanan da su ka samu. Daga nan kuma INEC ta gurfanar da shi gaban kotu.

Mr. Okoye ya ƙara da cewa a yanzu haka kuma INEC na ci gaba da zuwa shari’ar wani da aka kama da katin zaɓe har guda 367 a Kano.

Ya ce hukumar su za ta tabbatar da shi ma wannan ɗin sai an hukunta shi, kamar wanda aka ɗaure a jihar Sokoto.

Idan ba a manta ba, a jihar Kano ‘yan sanda sun Kama wani jigon APC mai suna Aminu Shana, ɗauke da katin rajistar zaɓe har guda 367.

Kunji fa menene ra’ayoyin ku game da wannan labarin?

Views: 4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *