Nasa naira miliyan50 ga duk wanda ya kawo Video-Audion inda nace Allah bai karɓar addu’ar talakan Najeriya—Atiku

Tsohon mataimakin tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo, Alhaji Abubakar Atiku ya sa kyautar naira miliya hamsin ₦50,000,000 ga duk wanda ya kawo Video ko Audion inda ya taɓa firta cewa Allah baya karɓar addu’ar talakawan Najeriya.

Idan ba’a manta ba wasu daga cikin ƴan ƙasar sun shafe lokutta masu tsawo suna ta yayata cewa mai girma wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ɗin ya ce Allah baya karɓar addu’o’in talakawan ƙasar.

Wanda suke zargin cewa ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake kan kujerar mataimakin shugaban Najeriya tsakanin shekarun 1999-2007, an dai ɗauki lokaci mai tsawon gaske ana ta yaɗa wannan labari wanda wasu ke amfani da shi.

A matsayin wani babban makamin farfagandar siyasa da nufin cimma wani buri nasu

Menene ra’ayoyin ku game da wannan batu?

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *