Ƴar Jaridar nan ta ƙasar Falasdinu wato Bushra ta shaƙi iskar ƴanci daga hukumomin Isra’ila

Hukumomin ƙasar Isra’ila sun saki ƴar Jaridar nan ta ƙasar Falasdinu wacce suka kama tare da tsare ta na tsawon watanni.

Bushra Ƴar jarida ta ƙasar falastin ta shaƙi iskan ƴancin daga kurku na ƙasar Isra’ila.

Bushra Taweel yar jaridar kasar Falastin, ta shaki iskar yanci jiya Lahadi bayan ta shafe tsawon watanni 9 a gidan yari na kasar Isra’ila.

Dama dai an jima ana zargin cewa ƙasar ta Israela ta yi ƙaurin suna wajen take haƙƙin bil’adama musamman Falasɗinawa.

A yanzu dai za a iya cewa ƴar jaridar ta samu cikakken ƴanci bayan da tayi ido huɗu da ahalinta kuma ana sa ran zata koma bakin aikinta nan ba da jimawa ba.

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *