Labari Da Ɗumi Ɗumi: “Kamfanonin bada lamuni a Amurka sun riƙe jirgin shugaban Najeriya”

Yawan bashin da ake bin Najeriya

Wata jaridar ƙasar Amurka mai suna NewsDay ta bada rahoton cewa kamfanonin bada lamuni na duniya dake bin Najeriya bashin kuɗi sun rubuta takarda zuwa ga gwamnatin ƙasar Amurka akan suna son.

Su tsare jirgin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuna su saka shi a kasuwa har sai Najeriyar ta biya shi bashin Dala biliyan 100 da suke binta.

YAWAN BASHIN DA AKE BIN NIGERIA YAKAI NAIRA TIRILIYAN 42.

Yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai sama da naira tiriliyan arba’in da biyu daga ƙarshen watan Yuni, kamar yadda ofishin kula da basusuka a Najeriya ya sanar.

Ofishin ya bayyana a cikin rahoton da ya fitar ranar Laraba cewa yawan bashin ya ƙaru da naira tiriliyan 2.38 tsakanin wata uku.

Yawan bashin ya shafi wanda jihohi da gwamnatin tarayya suka karɓo.

“Alƙalumman sun nuna cewa a naira – jimillar bashin na gwamnatin tarayya da jihohi 36 haɗi da Abuja ya kai naira tiriliyan 31.009 kwatankwacin dala biliyan 85.897.

Bashin ya ƙaru ne saboda rancen dala biliyan 3.36 da gwamnati ta karɓo daga asusun lamuni na duniya IMF da kuma rance daga cikin gida don tallafawa kasafin kuɗi na shekarar 2020 da aka sabunta.

Daga ƙarshen 2015, bashin naira tiriliyan 12.12 ake bin Najeriya, makwanni bayan hawan gwamnatin APC ta shugaba Buhari.

Hakan na nufin tsakanin shekaru biyar na mulkin Buhari, bashin Najeriya ta ƙaru da kusan tiriliyan 19. Ofishin kula da basussuka a Najeriya ya ce yawan bashin zai ƙaru yayin da ake jiran kusuka.n rance daga Bankin Duniya da Bankin raya Afirka da kuma Bankin musulunci domin tallafawa kasafin kudin Najeriya na 2020 musamman wanda ƙasar ta nema sakamakon tasirin annobar korona.

An dai bayyana cewar idan ana son a biya bashin da ake bin Najeriya ko wane ɗan ƙasar sai ya bada kusan ₦200,000.

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *