VIDEO: “Hukumar Hisba na neman Abdul Babulaye kan wannan bidiyon”

Hukumar Hisba na neman jarumin fina finan Hausa Abdul Babulaye Wanda ke sakin bidiyon barkwanci a kafafen sada zumunta na zamani.

Matashinnan wanda ya yi ƙaurin suna wajen sakin bidiyon barkwanci wani lokacin hadda na batsa mai suna Abdul Babulaye ya fitar da wani bidiyon da bai dace ba.

Ana zarginsa da yin kalamai na banza waɗanɗa basu dace ba, a koyarwar addinin Musulunci dama al’adar malam bahaushe.

Dama dai tuni ake kiraye kirayen cewa ya kamata a taka masa burki kan irin abubuwan da yake yi a shafukan yanar gizo.

Mabiya shafukansa na sada zumunta tsakanin samari da ƴan mata sun jima suna ƙorafin cewa bai dace a zuba masa ido yaci gaba da yin abinda yake yi ba.

Baya ga Abdul Babulaye itama kararriyar tsohuwar jarumar shirun Kwana Casa’in wanda ake haskawa a tashar talabijin ta Arewa24 wato Safeeya Yuseef wacce ake yiwa laƙabi da sunan Safara’u.

Tana ɗaya daga cikin waɗanda hukumar ta Hisba ta bada umarnin kamo su a duk inda suke sakamakon yin raye raye da waƙoƙin batsa waɗanda ake zargin suna aikatawa.

Shima dai ogan na Safara’u wato mista 442 yanzu hakan batun da muke yana can tsare a hannun hukumomin ƙasar Nijar bisa samunsa da laifin keta haddin dokar ƙasa.

Yanzu haka dai batun da ake yana can kulle tare da abokinsa Mr. Ola wanda ake yi wa laƙabi da suna Ola of Kano bisa samun su da laifin mallakar katin zama ɗan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko gwamnatin ƙasar ta jamhuriyar Nijar za ta sassauta musu ta sake su domin su dawo ƙasar su ta asali wato Najeriya.

Wannan mataki na hukumar Hisba na kama mawaƙan hausa dai wasu na ganin bai kanata ba yayi da wasu ke ganin dai dai ne ku manene ra’ayoyin ku?

Views: 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *