Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi fatan samun Shugaba na gari ga ƙasar a kakar zaɓen 2023 a jawabinsa na sabuwar shekara Buhari ya gargaɗi ƴan ƙasar da su zage damtse su zaɓo shugaba na gari wanda zai ɗora daga inda zai tsaya.
Bugu da ƙari Shugaban yace zai umarci babban bankin ƙasar na CBN ya rabar da kuɗaɗen daya tara ga ƴan ƙasar don rage raɗaɗin talauci da tsadar rayuwa.
A wani rahoton kuma
Gwamnatin Zamfara Za Ta Ɗauki ‘Yan Sa-kai 2000 Don Yaƙar ‘Yan Bindiga
Daga Abbakar Aleeyu Anache
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta amince da daukar sabbin mayakan sa’kai dubu 2 don shiga cikin rundunar yaki da ‘yan bindigar wadda gwamnatin jihar ke tafiyarwa a kokarin baiwa jama’a cikakkiyar kariya daga batagarin.
Shugaban kwamitin da ke kula da dakarun masu yaki da yan bindigar a Zamfara Mr Bello Bakyasuwa a jawabinsa gaban manema labarai a ranar Alhamis da tagabata a birnin Gusau ya ce sun karbi umarnin daga gwamna Bello Matawalle game da daukar sabbin yan sa’kai.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ne ya yi umarnin kafa kwamitin na musamman don yakar matsalolin yan ta’adda da garkuwa da mutane da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.
A cewar Bello Bakyasuwa akalla mutane dubu 6 da 700 suka mika takardun neman aikin a sassan jihar ciki har da mata sai dai duka-duka mutum dubu 2 za a dauka don gudanar da aikin,
Jihar Zamfara na sahun jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar yan ta’adda da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Views: 14
