
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Daga APC AREWA CONCERN FORUM
Shahararriyar ƙungiyar nan ta APA Arewa Concern Forum, ta fitar da sanarwar janyewa daga duk wasu ayyukan siyasa da suke da alaƙa da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) da ɗan takar ta na shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tunubu a dukkan sassan jihohin ƙasar nan 36 harda Abuja fadar gwamnatin tarayyar Najeriya.
Ƙungiyar mai haɗakar ƙungiyoyin siyasa 2,000 a faɗin jihohi 36 harda Abuja na sanar da duniya cewa ba zata bawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tunubu ƙuri’u million 6 da take dasu a faɗin ƙasar nan a zaɓen 2023 mai zuwa.
Sakamakon rashin daraja ta da uwar jam’iyyar APCn ta ƙasa ke yi.
Wannan sanarwar ta fito ne daga shugabannin ƙungiyar na ƙasa a yau 27 ga watan Disamba bayan sun gudanar da taron su da dukkan ƙungiyoyin da suke tare da su a jihar Kaduna.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta na sanar da dukkan jama’a cewa za ta fitar da sanarwa ta gaba domin bayyana makomarta a taron manema labarai na ƙasa da ƙasa da zata gudanar nan gaba kaɗan.
Views: 3
