Wani hoton bidiyo ya nuna yadda al’ummar ƙaramar hukumar Kankia dake a jihar Katsina ke yin ihu ga tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyar APC.
A ɓangare guda kuma magoya bayan Atiku sun yi tsokaci gane da hana su gudanar da yaƙin neman zaɓensu a filin ƙallon Karkanda kafin daga bisani a barsu ga abinda Malam Datti ke cewa.
SUN HANA ATIKU GURIN TARO
Gwamnan jihar Katsina ya hana Maigirma Shugaban Nigeria mai jiran gado Insha Allah Alhaji Atiku Abubakar gurin da zai gudanar da taron kamfen dinsa gobe Talata a jihar Katsina
A fahimtata tsoron jin kunya ne yasa Gwamnan Katsina ya hana Atiku gurin taro, saboda ba shakka Gwamnatin APC taci amanar talakawan jihar Katsina, ta gaza wajen basu kariya daga masu satar mutane, kuma abin takaici jihar Shugaban Kasa
Gobe Atiku da tawagarsa zasu isa jihar Katsina da ikon Allah, ko a jeji ne Atiku zai yi kamfen dinsa, kuma sai ya bada makaki da ikon Allah
Yaa Allah Ka nuna mana karshen mulkin APC a 2023 lafiya
Views: 7
